✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga Sun Kashe Manoma A Cikin Gona a Kaduna

A shekarar da ta gabata ’yan bindiga sun sassari mahaifin manoman a cikin gona

Manoma a yakin Zariya sun fara fuskantar rashin kwanciyar hankali na matsalar tsaro a daidai lokacin da suka himmatu wajen aikata gonakinsu saboda saukar ruwan sama.

A ranar Talata ne wasu ’yan fashin daji suka harbe wasu samari biyu a lokacin da suke shuka a gonarsu da ke Iyatawa a Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

Samarin wadanda ’yan uwan juna ne, Alhaji Mustapha Lawal da Bello Lawal, mazauna Kofar Jatau da ke cikin Zariya ne.

Aminiya ta samu bayani cewa a daminar shekarar da ta gabata ne mahaifin matasan ya sha da kyar bayan ’yan bindiga sun sassare shi, wanda hakan ta sa ya yi fama da jinya.

Manoman da Aminiya ta zanta da su, sun bayyana cewa baya ga rashin tsaro, suna fama da tsadar rayuwa da tsadar takin zamani da duk wani kaya da ya shafi aikin gona.

Sun kara da cewa a wuraren da ake zaune lafiya kuma, “Idan ka nemi inda za ka dan noma, tun da noma shi ne sana’ar, sai ka ji kudin hekta daya ya kai N80,000 ko N100,000.

“Don haka maganar noma a wannan lokacin sai abin da Allah Ya yi,” amma suna rokon Allah Ya kawo mafita.