✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutane 21, sun yi garkuwa da 40 a Neja

'Yan bindigar sun farnaki kauyuka uku a jihar Neja.

Akalla mutane 21 ne aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da kimanin 40 a wani a sabon hari da ’yan bindiga suka kai a Karamar Hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa wakiliyarmu, cewa ’yan bindigar da adadinsu ya kai kusan 300 sun farmaki kauyukan Kurege da Sabon Gida da Sararai da Rafin Kanya a ranar Litinin, a kan babura inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.

’Yan bindigar sun kuma kashe mutane da dama sannan suka yi garkuwa da wasu.

Malam Galadima Salisu, daya daga mazauna yankin ya bayyana fargabarsa kan yadda ‘yan bindiga suka addabi yankin.

Ya ce matukar gwamnati ba ta kai musu dauki ba, akwai yiwuwar ’yan bindigar su kwace yankin ya koma karkashin ikonsu.

Sai dai kokarinmu na samun Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun don jin ta bakinsa kan harin ya ci tura.

Sakataren Gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da faruwar harin, sai dai bai bayyana adadin mutanen da aka yi garkuwar da su ba.

Matane ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar na iya kokarinta wajen kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi jihar.