Akalla mutum uku ne ‘yan bindiga suka kashe suka kuma jikkata wasu ukun a harin da suka kai da tsakar dare a Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina.

Mazauna kauyen Marar Zamfarawa sun ce ‘yan bindiga sun far wa kauyen bayan karfe 12.00 na dare inda suka yi ta musayar wuta da jami’an tsaron sa-kai da na gwamnati.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta ce mutum biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon harin na ranar Juma’a.

Mazauna kauyen sun ce an garzaya da wadanda aka raunata zuwa Babban Asibitin Danmusa inda ake jinyar su, bayan an yi jana’izar wadanda suka rasu da safiyar Asabar.

Yankin Danmusa na daga cikin sassan jihar Katsina da ke yawan fama da matsalar mahara masu karkashe mutane da kuma yin garkuwa da su.

Kimanin mutum 100 ne maharan suka kashe a yankunan a baya-bayan nan baya ga wadanda suka yi awon gaba da su.