✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Filato

An baza jami'an tsaro a yankin don bin sahun maharan.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta ce ’yan bindiga sun kashe mutum 10 a yankin Sabon Layi da ke Kuru a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Ubah Ogaba, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Jos a ranar Litinin.

  1. Zaben 2023: Fastocin Tinubu sun mamaye birnin Abuja
  2. Wata mata ta sayar da ’ya’yanta biyu a Ogun

“Mun samu rahoton kashe mutum 10 da wasu ’yan bindiga suka yi a wata mashaya da ke Sabon Layi a Kuru Jos ta Kudu.

“Tuni aka tura jami’an tsaro yankin don yin bincike tare da gano wadanda suka aikata hakan.

“Kwamishinan ’Yan Sanda ya ba da umarnin bincike tare da cafke wanda suka kai harin,” cewar Ogaba.

Wani ganau ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), cewar mutum 12 ne suka rasa ransu, wasu biyar kuma suka samu raunuka a sakamakon harin.

“Na lissafa mutum 12 da suka rasu da hannuna sannan biyar sun ji rauni.

“Wanda suka ji raunin suna wani asibiti da a bayyana sunansa ba ana ba su kulawa,” cewar wanda ya ganewa idonsa faruwar harin.