✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 14, sun kone gidaje 56 a Kaduna

'Yan bindigar sun kuma kone gidaje da baburan mutane da dama.

Mutum 13 ne ciki da har yaro mai shekara daya a duniya aka kashe bayan wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a Kananan Hukumomin Zangon Kataf da Kauru da Chikun a jihar Kaduna.

Aminiya ta gano cewa an kuma kone gidaje 56 da babura 16 a yayin hare-haren.

Baya ga wadanda aka kashe, ‘yan bindigar Sun kuma ji wa wasu ƙarin mutum uku munanan raunuka.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar harin ranar Juma’a.

Sai dai ya ce tuni aka tura jami’an tsaro yankunan da hare-haren ya shafa don kai musu dauki.

Samuel Aruwan ya kuma ce Gwamnan Jihar Mallam Nasir El-Rufai, ya nuna damuwarsa tare sa jajantawa iyalan wadanda harin ya ritsa da su tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun waraka.