✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 15 a kauyen Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun halaka mutum 15 a kauyan Gonar Rogo a gundumar Kufana da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna. Lamarin ya faru…

Wasu ’yan bindiga sun halaka mutum 15 a kauyan Gonar Rogo a gundumar Kufana da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na daren Litinin.

Maharar sun sace shanu tara sannan suka raunata wasu, a yanzu haka wadanda suka samu rauni suna jinya.

Rahotonni daga yankin sun ce, akalla mutum 15 ne suka rasu wasu kuma sun jikkata. Maharar sun kwashe shanu tara kafin su fice daga cikin kauyan.

Shugaban karamar hukumar da Hakimin Kufana da sauran jami’an tsaro sun ziyarci yankin.

Buhari ya yi Allah wadai da harin Kajuru

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da abin da ya bayyana “hare-haren ramuwar gayya a yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani sakon tiwita da ya wallafa cikin daren ranar Talata, inda  ya ce ba daidai ba ne kisan gilla da sunan ramuwar gayya.

Buhari ya yi Allah wadai game da hare-haren  ramuwar gayya tsakanin kabilun yankunan Kajuru.