✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 15 a kauyen Kaduna

Maharan sun kashe mututum 15, suka kuma kone kantuna da motoci.

’Yan bindiga sun farmaki kauyen Kaya da ke yankin Fatika a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum 15 tare da kone kantuna 11 da ababen hawa biyar.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun kai harin da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar.

Wasu mazauna yankin na zargin ganin harin ramuwar gayya ce a kan wani mazaunin yankin, wanda suka ce an kashe masa ’yan uwa guda uku.

Mazauna kauyen Kaya

Ibrahim Ahmed Fatika, ya shaida wa Aminiya a safiyar Lahadi cewa, takwas daga cikin wanda aka kashe mazauna kauyen Kaya ne, ragowar bakwan kuma, ciki har da wani direban Tirela, baki ne.

Ahmed ya ce an yi jana’izar mutane takwas din da aka kashe da safiyar ranar.

Sannan a cewarsa an jibge jami’an soji guda 10 a kauyen domin ba wa mutanen kauyen tsaro.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kone motoci guda uku, da kuma shagunan sana’ar kafintoci.

Shagunan da ‘yan bindigar suka kone

Wani mazaunanin kauyen, Abdu Sa’idu, ya ce harin na da alaka da kone gidan wani da ake kira Filani, wanda aka kashe wa ’yan uwansa har uku.

Ya kara da cewa ’yan bindigar sun yi garkuwa da mutum biyar ciki har da wata amarya a kauyen Kaura.

Daya daga cikin motocin da aka kone

Rundunar ’yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce an kashe mutum takwas.

Kakakinta, ASP Mohammed Jalige, ya ce mutanen kauyen sun yi kuskuren farmakar mutanen da suke zargi da ayyukan ’yan bindiga ba tare da sun sanar da hukuma ba.

Jalige ya kara da cewa an aike da karin jami’an ’yan sanda yankin.

Shugaban Karamar Hukumar, da wasu daga masu wakiltar yankin sun kai ziyara kauyen domin jajanta musu.