✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 2, suka sace mutum 10

'Yan bindigar sun tsayar da wata mota kirar bas inda suka yi garkuwa da mutane 10.

Akalla mutum biyu sun mutu a wani fashi da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutum 10 a Jihar Edo.

Lamarin ya faru ne a garin Obagie da ke kan hanyar Benin-Ekpoma-Auchi a Karamar Hukumar Uhunmwonde ta jihar ranar Laraba.

Wata majiya ta ce mamatan sun hada da wani dan banga da wani fasinjan da ke cikin motar bas din da ’yan bindigar suka tare suka kuma yi amfani da ita suka toshe hanyar.

An gano cewa ’yan bindigar wadanda suka fito daga daji sun bude wa motar bas din wuta ne suka tilasta mata tsayawa sannan suka tasa keyar mutum 10 zuwa cikin daji.

Majiyar ta ce wata babbar mota da ta ki tsayawa a lokacin da ’yan bindigar suka tsayar da ita, ta kashe mutum daya, inda ya bi ta kan bas din da suka tare hanya da ita.

Mutane da dama da suka biyo hanyar sun tsere sun bar ababen hawansu domin tsira da rayuwarsu.

Majiyarmu ta shaida wa wakilinmu cewa an yi garkuwa da mutum 10 amma an baza jami’an tsaro a kan hanyar bayan faruwar lamarin.

Sai dai wakilinmu bai samu tattaunawa da kakakin ’yan sandan jihar SP Chidi Nwanbuzor ba, domin jin ta bakinsa game da faruwar lamarin.