’Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Kaduna | Aminiya

’Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
    Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna da Sagir Kano Saleh

’Yan bindiga sun kashe akalla mutum 20 a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Maharan sun rika banka wa gidaje da motoci da amfanin gona a gonaki wuta a wasu kauyuka uku.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da harin a ranar Lahadi.

Ya ce an kai hare-haren ne a kauyukan Kauran Fawa da Marke da kuma Riheya da ke yankin Idasu.

Aruwan ya bayyana ta’aziyyar Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai ga iyalan mamatan tare da umartar Hukumar Ba Da Agaji ta Jihar ta kai musu tallafi.