✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 28 a Sakkwato

’Yan bindiga sun kashe mutum 28 tare da sace wasu da sama a kauyen Duma na Karamar Hukumar Tureta ta Jihar Sakkwato

’Yan bindiga sun kai wani mummunan hari a kauyen Duma da ke Karamar Hukumar Tureta ta Jihar Sakkwato, inda akalla mutum 28 suka rasa rayukansu.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana adadin wadanda suka rasa rayukansu a ranar Juma’a bayan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar jaje a kauyen.

Rahotanni sun bayyana cewa, harin ya faru ne tun a daren ranar Laraba, inda maharan suka mamaye kauyen tare da yin gaba da mutane da kuma dabbobi da dama.

Wani mazauni kauyen mai suna Garba Mailambu ya shaida wa manema labarai cewa, ’yan bindigar sun zo ne a kan babura suna ta harbi kan mai uwa da wabi.

Ya Kara da cewa wasu mazauna kauyen sun afka a cikin gulbi a yayin gudun tsira da rayukansu, wasu na ciki wasu sun fita.

Shi ma wani mazauni kauyen ya bayyana cewa maharan sun tafi da wadanda suka yi garkuwa da su, mafi yawansu matasa ne domin su kora musu dabbobi zuwa wajen gari.

Haka kuma maharan sun bukaci man fetur mai yawa a matsayin kudin fansa domin sako wadanda suka yi garkuwa da su.

A ziyarar Tambuwal bayan ya jajanta wa mutanen kauyen, ya roki a bai wa jami’an tsaro goyon baya da yin addu’ar samun nasara ga tarwatsa bata-garin.

Ya roki al’umma su bayyana mutanen da ke ba da bayani ga ’yan bindigar, “Komai alakar da take tsakaninka da mai ba da kwarmaton hakan zai taimaki tsaro a cikin al’umma.”

Tambuwal ya umarci a fitar kayan agajin gaggawa ga ’yan gudun hijira da ke yankin.