✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 3 a Katsina

Bayan kashen mutum uku, sun sace mai unguwar yankin.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyuka hudu na Karamar Hukumar Funtua ta jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutum uku.

Maharan da sun kai su dari, an ce sun kai farmaki kauyen Yartafki da ke kan titin Funtua zuwa Zariya da misalin karfe 11:00 na daren Litinin.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da wani Malam Bala Magaji, Shugaban Karamar Sakandaren Gwamnati da ke Makera a garin na Funtua.

A cewar dan uwan ​​shugaban makarantar da aka sace, ‘yan bindigar sun shiga kauyen Unguwar Isiyaka ne da misalin karfe 11:15 na dare, inda nan ma suka fara harbe-harbe har suka kashe wasu matasa uku.

“Hare-haren da aka kai a kauyukan hudu kusan lokaci guda ne; sun kashe Samaila Badamasi mai shekara 40, Malam Abdulkadir Adamu mai shekara 35 da Naziru Tasi’u dan shekara 25.

“Sun yi garkuwa da mutum takwas da suka hada da yayana da Hakimin unguwarmu, Mai unguwa Kabiru,” inji shi.

Ya kara da cewa, a cikin daren ne ‘yan bindigar suka sako hudu daga cikin wadanda suka sace wadanda matasa ne kuma suka yi garkuwa da tsofaffi.

Sun yi awon gaba da babur guda daya tare da wawushe wasu dukiya a wasu shaguna a kauyen.

A garin Zagamawan Kwari a cewar Sufi Usman Danbaure, ‘yan bindigar sun harbe wani Alhaji Saminu tare da raunata wani mutum daya, sannan sun yi awon gaba da matan mahaifinsa guda biyu.

“A unguwar Sallah ba su kashe kowa ba amma sun yi awon gaba da babura biyu,” cewar Danbaure.

Ya kara da cewa, mazauna unguwar Sanga, unguwar Cibauna, Kaliyawa da wani bangare na Gwaigwaye sun yi kaura daga gidajensu saboda fargabar harin ‘yan bindiga.

“Hare-hare na baya-bayan nan a yankunan na haifar da babbar barazana ga ayyukan noma.”

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce zai yi bincike a Karamar Hukumar da abin ya shafa don tabbatar da faruwar lamarin.