✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 12 a Suleja

’Yan bindigar sun rika bi gida-gida suna yin awon gaba da mutane.

Masu garkuwa da mutane sun kashe mutum uku suka kuma sace wasu 12 a Karamar Hukuamr Suleja ta Jihar Neja.

’Yan bindigar sun far wa unguwar Kwankwashe da ke garin Suleja ne suna harbe-harbe da tatainin dare, lamarin da ya sa mazauna gudun neman tsira.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun rika shiga gida-gida suna tisa keyar mutanen da ba su yi maza su tsere ba a lokacin harin na daren Alhamis.

Daga cikin mutanen da suka kashe har da karamin yaro mai shekara shida, kazalika akwai kananan yara a cikin wadanda suka sace.

Mazauna unuguwar sun ce masu garkuwa ba su tuntubi iyalan wadanda aka sace ba tukuna, amma an sanar da jami’an tsaro abin da ya faru.

’Yan bindiga sun sha kai hari tare da yin garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Suleja.

Amma mazauna sun bayyana damuwa kan rashin bazuwar labarin hakan, inda aka fi mayar da hankali a kan Kananan Hukumomin Munya da Shiroro da Rafi.

An nemi mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, domin karin bayani amma wayarsa a kashe, bai kuma amsa rubutaccen sakon da aka aika masa ba.