✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 6 a Katsina

Daga cikin wadanda maharan suka sace har da wata mata mai juna biyu.

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun kashe mutum uku a kauyen Jajar kanwa da ke Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina, yayin da suka yi awon gaba da mutum shida ciki har da wata mai juna biyu.

Mazauna yankin sun ce cikin mutanen uku da aka kashe har da wata mace daya a wani asibiti a kauyen.

Kazalika, maharan sun kuma yi awon gaba da awaki da tumaki da ba a tantance adadinsu ba bayan sanya harajin Naira dubu 20 kan kowane mazaunin garin.

A zantawar da suka yi da wakilinmu ta wayar tarho, wasu mazauna unguwar sun ce dole ne a biya harajin Naira 20,000 a cikin mako guda ko kuma su sake kai wani harin.

A wani labarin mai nasaba da wannan, wasu da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Musawa a Jihar Katsina, Aminu Umar Kira a gidansa.

Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani game da sace shi, amma wani mazaunin garin ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, sai dai lamarin ya ci tura.