✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace wasu 36 a Kaduna

An yi awon gaba da mutum 22 a harin da aka kai a unguwar Idon Hanya

’Yan bindiga sun kashe mutum uku suka kuma yi garkuwa da wasu 36 ciki har da wani kansila da mai unguwa a Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da hakan, Hakimin Kufana, Titus Dauda, ya ce al’ummar sun kira sojoji su kawo musu dauki, amma ’yan bindigar suka yi wa sojojin kwanton bauna suka fasa tayar motar sojojin.

“Mun shiga tashin hankali saboda an kawo harin ne da misalin karfe 12 na dare aka kashe mana mutum uku aka yi garkuwa da wasu uku,” inji shi.

Ya ce A ranar Litinin ’yan bindigar sun kai harin ne a ranar 14 zua 15 ga watan Fabrairu inda suka yi awon gaba da mutum 22 a unguwar Idon Hanya.

Sun kuma sace mutum shida da unguwar Tudun Mare suka kashe mtuum daya bayan wasu mutum shida da akak yi garkuwa da su a unguwar Afogo.

A kauyen Rimau an sace mutum biyu ciki har da wani kansila da mai unguwa, sannan ’yan bindigar suka kashe dan kansilan mai shekara 10.

Mun tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, domin samun karin bayani, amma ya yi alkawarin bincikawa sannan ya yi mana bayani,.

Sai dai kuam har har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoton babu labari.