✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 4 a Bauchi

Hare-haren dai sun jefa mazauna yankin cikin firgici matuka

Wasu mahara da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe mutum hudu suka sace wani sannan suka jikkata mutum daya a gundumar Burra da ke Karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi.

Hare-haren dai sun jefa mazauna yankin cikin firgici matuka.

Rahotanni sun ce maharan sun farmaki kauyukan Yadagungume da Limi inda suka kashe mutum uku, bayan awa 24 suka kai hari kauyen Agwarmaji, suka kashe mutum daya.

Wasu mazauna yankin, Sadam Mato, Fatima Sani da Iliya Haruna, sun shaida wa manema labarai a Bauchi cewa tuni aka binne mutane hudun da aka kashe kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mutum guda yana karbar magani a asibiti.

Ya ce an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda a ranar Laraba da misalin karfe 5:00 na safe.

Ya ce, “Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai farmaki kauyen Yadagungume, inda suka harbe mutum biyu daya, Shu’aibu Sani, mai shekaru 25, da kuma Ruwa Ali, mai shekaru 35, dukkansu maza ne da ke zaune a kauyen Limi ta unguwar Sama, yayin da wani Yusuf Sani mai shekaru 30 daga Yadagungume, ya samu raunuka a jikinsa, kuma an garzaya da shi Babban Asibitin Ningi, a yanzu haka yana kan karbar magani.”

Kakakin ’yan sandan ya ce ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wani matashi mai suna Shuaibu Bala mai shekaru 26 a unguwar Yadagungume zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wakil ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa kuma Baturen ’Yan Sanda na yankin Burra (DPO) na sashen Burra ya jagoranci tawagar ’yan sanda suka je wurin da lamarin ya faru, inda aka samu kwanson harsashi AK-47 guda 13 yayin da ake zargin da su ne wadanda ake zargin sukayi amfani dasu.

Ya ce an kai gawarwaki biyu asibiti da ke Yadagungume domin duba lafiyarsu, inda likita ya tabbatar da mutuwarsu, sannan aka mika su ga iyalansu domin yi musu jana’iza.

“Daya daga cikin wadanda abin ya shafa da na ambata a sama an yi garkuwa da su, daga baya aka same shi da harsashi a jikinsa. Shi ma an kai gawarsa asibiti, har yanzu muna jiran rahoton lafiyarsa.”