✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 4 a Kaduna

Jami'an tsaro sun yi nasarar ceto dukkanin matan da aka yi garkuwa da su.

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutane hudu yayin da suka kai hari kauyen Katarma dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Rahoton ce bayan wani dauki ba dadi da ’yan banga a kauyen, ’yan bindigar sun kuma sami nasarar yin garkuwa da wasu mata.

Sai dai a yayin artabun, ’yan bindigar sun kashe mutane hudu, tare da raunata wasu uku a kauyen.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce an kubutar da ilahirin matan da aka yi garkuwa da su daga bisani.

Ya kara da cewa sojin sama sun kai hari a dajin kauyen na Katarma da na Kusasu a kan ‘yan bindigar.

A sakamakon harin a cewar Kwamishinan, sojojin sun yi nasarar kashe da dama daga cikinsu, yayin da wasu da dama suka tsere.