✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sun kashe mutum 4 bayan karbar kudin fansa N60m

Masu satar mutane sun harbe wasu matasa da suka yi garkuwa da su hudu har lahira, bayan karbar kudin fansa Naira miliyan 60. Lamarin ya…

Masu satar mutane sun harbe wasu matasa da suka yi garkuwa da su hudu har lahira, bayan karbar kudin fansa Naira miliyan 60.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi  a wani daji da ke kusa da Garin Dogo da ke Karamar Hukumar Lau ta jihar.

Rahotanni na nuna cewa matasa uku daga ciki ’yan gida daya ne, kuma mahaifinsu ne ya yi magan da wadanda suka sace shi, har suka amince da karbar N60m madadin N100m da suka bukata a matsayin kudin fansa.

Sa dai bayan samun dan acaban da ya tura ya kai musu kudin dajin, sai suka harbe matasan har lahira a kan idonsa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an dauko gawarwakin matasan an kuma binne su.