✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 60 ‘yan bindiga suka kashe a Katsina — Mazauna

‘Yan bindiga sun kashe akalla mutum 60 a kananan hukumomin Faskari, Sabuwa and Dandume na jihar Katsina, a cewar mazauna kauyuka. A cewarsu, maharan sun…

‘Yan bindiga sun kashe akalla mutum 60 a kananan hukumomin Faskari, Sabuwa and Dandume na jihar Katsina, a cewar mazauna kauyuka.

A cewarsu, maharan sun mamaye kauyukan Faskari, inda suka kashe mutum 40, suka yi wa jama’a fashi, suka kona gidaje da rumbuna sannan suka saci dabbobi.

“Maharan wadanda akasarinsu ke kan babura sun mamaye yankunan tare da cin zarafin ‘yan mata da ma matan aure”, wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar PRNigeria. 

Kauyukan da harin ya shafa sun hada da Kadisau, Maigora, Kabalawa, Raudama, Kwakware da Unguwar Wahabi.

‘An kashe mutum 32 a Kadisau’

Mazauna Kadisau sun ce ‘yan bindigar sun kashe mutum 32 tare da raunata wasu 25 bayan sun shafe kusan sa’a uku suna barna.

Maharan a cewarsu sun fara bude wuta ne a kan matasa da ke wasan kwallo kafa da yammaci, sannan sauka bi gidaje suna bude wuta.

“Sai wurin 8.00 na dare suka bar Kadisau. Sun zo a babura kusan 150 kowanne da goyon fiye da mutum biyu.

Ya ce an kashe mutum 32 a Kadisau, 9 kuma a Hayin Kabalawa. “Da safiyar yau (Laraba) muna shirin binne su sai muka samu labarin ‘yan bindigar sun kai wa makwabtanmu hari.

“Dole ta sa muka tsere domin neman mafaka, amma yanzu sojoji sun zo domin bayar da kariya mu samu mu binne ‘yan uwanmu.

An yi kari a labarin — ‘Yan sanda

Sai dai Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsinar ta ce mutum 20 ne aka kashe a hare-haren da ‘yan bindigar suka kai kananan hukumomin uku.

Kakakin rundunar, SP Sabo Isah ya kuma karyata labarin harin ‘yan bindigar a wurin jana’iza a kauyen Kadisau.

Ya kara da cewa baturen ‘yan sanda na shiyyar Funtua tare da hadin gwiwar sojoji suna nan sun dukufa wajen ganin an yi jana’izar lami lafiya da ma bayan hakan.

Masari ya janye sulhu da ‘yan bindiga

Hare-haren na zuwa ne kwana biyu bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umurci sojoji da sauran jami’an tsaro da su kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Kazalika Gwamna Aminu Masari ya janye sulhun da gwamnatinsa ta yi da ‘yan bindigar, wadanda ya ce sun dade suna saba yarjejeniyar da aka yi da su.

Masari ya ce gwamnatinsa za ta dauki matakin ba sani ba sabo kan maharan saboda sun bijire wa kokarin samar da zaman lafiya a jihar.

A baya-bayan nan matsalar tsaro da hare-haren ‘yan bindiga na kara yawaita a jihar Katsina inda a wasu lokuta maharan ke garkuwa da mutane.

Ko a ranar Talata dai sai da wasu fusatattun matasa a garin ‘Yan-Tumaki suka yi zanga-zangar nuna bacin ransu kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ta sanadiyyar rayuka da dukiyoyin al’ummar yankunansu.