✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 40 a kauyukan Zamfara

’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da shanu da tumaki yayin harin.

Wasu ’yan bindiga sun hallaka akalla mutum 40 bayan wasu hare-hare da suka kai gundumar Faru da ke Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Hare-haren dai wadanda aka kai su da daren ranar Alhamis sune na baya-bayan nan da ’yan bindigar ke kai wa kauyukan Jihar a kan babura.

Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Gudan Baushi da Gidan Adamu da Tsauni da Gudan Maidawa da kuma Wari.

Mazauna yankunan sun shaida wa Aminiya cewar ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da shanu da sauran dabbobi lokacin da suka rika bi gida-gida yayin harin wanda ya dauki tsawon sa’o’i.

A cewa Haruna Halilu, wani mazaunin yankin, “Manoma da dama an yi musu kofar rago a gonakinsu. Jami’an tsaro da taimakon ’yan kato-da-gora na ta kokarin debo gawarwakin wadanda aka kashe daga cikin dazuka.

“Wasu manoma sun riga sun tafi gona basu san cewa ’yan bindigar na can suna cin karensu ba babbaka ba. Wasu daga cikin manoman na tafiya da bindigoginsu zuwa gonakin domin kare kansu.

“Yanzu haka ana nan ana shirin binne su a kauyen Faru wanda shine mafi girma, saboda tsoron kada su sake dawowa su kai hari kan masu jana’izar,” inji Haruna.

Sai dai yunkurinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sanda reshen Jihar, SP Mohammed Shehu ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.