✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Jihar Binuwai

Akalla mutane biyar ne 'yan bindiga suka hallaka da sanyin safiyar ranar Lahadi a wurere daban-daban a

Akalla mutane biyar ne ‘yan bindiga suka hallaka da sanyin safiyar ranar Lahadi a wurere daban-daban a kananan hukumomi biyu dake jihar Binuwai.
Wakilinmu ya rawaito cewa ‘yan bindigar sun yi kutse ne cikin gidan tsohon dan majalisar jihar mai wakiltar Karamar Hukumar Katsina-Ala ta gabas dake kauyen Nagu, Inna Jato inda suka kashe uku daga cikin mutum biyar din.
Ragowar biyun ana zargin kisan nasu na da alaka da ‘yan kungiyar asiri a yankin Naka cikin karamar hukumar Gwer ta Arewa.
Wadanda lamarin ya faru akan idonsu, sun bayyana cewa ‘yan ta’addar sun kai wasu farmakin a wasu wurare biyu, inda suka lalata dukiyoyi da kona gidaje da dama, ciki har da gidan tsohon dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Katsina-Ala.
Jami’in Watsa Labaran Shugaban Karamar Hukumar Katsina-Ala, Tertsea Benga, ya tabbatar da kisan mutane ukun da ‘yan bindigar suka kashe a gidan tsohon dan majalisar jihar.