✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a kauyen Kaduna

’Yan bindigar sun kashe wani karamin yaro mai fama da tabin hankali.

’Yan bindiga sun kashe mutanen biyar a lokacin da suka kai hari kauyen Ganin-Gari da ke unguwar Randagi a Yammacin Karamar Hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

An kai harin ne a ranar Lahadi inda ’yan bindiga kusan 40 a kan babura suka afka wa al’ummar kauyen.

Aminiya ta gano cewa tun da misalin karfe 2:00 na rana mutanen yankin suka fara ganin ’yan bindigar na fitowa daga maboyarsu ta Kudancin dajin Kamuku ta Kurgan ta Gabas a Tudun Wada, da Unguwan Danbaki na unguwar Kakangi, inda suka nufi unguwar Ganin-Gari kai-tsaye.

Sun kashe mutum biyu, sun saci shanu sannan suka yi awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba.

Shugaban Kungiyar Masarautar Birnin Gwari, Ishaq Usman Kafai, ya ce mahara kusan 40 ne suka kai farmakin a kan babura a ranar Lahadi.

Ya ce sun kashe mutane biyu tare da kora shanu da kuma garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba a kauyen.

Kafai dai ya ce rundunar tsaron hadin guiwar ’yan sa-kai da ke kusa da gadar Tudun Wada sun kwato dukkanin wadanda aka sacen da kuma shanun da suka kora.

“A hanyarsu ta komawa maboyarsu sun kashe wani yaro mai tabin hankali da suka ci karo da shi a kan titi a kusa da kauyen Dawakin Bassa.

“Sannan a ranar Litinin sun kashe wasu mutane biyu a gona, wanda jimilla ya zama mutane biyar ke nan”, in ji shi.

A cewarsa, yankin yammacin Birnin-Gwari na fuskantar hare-hare daga ’yan bindiga inda hakan ya sa jama’a da yawa suka bar muhallansu.

Kungiyar ta kuma yaba wa ’yan sanda da ’yan banga na yankin bisa kokarinsu na kishin kasa tare da yin kira ga gwamnati da ta tura karin jami’an tsaro da isassun kayan aiki domin rage yawan ayyukan ta’addanci a yankin.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Muhammed Jalige, ba a samu damar jin ta bakinsa ba saboda lambar wayarsa ba ta shiga ba.

Kuma bai amsa sakon da aka aike masa ta WhatsApp ba a lokacin hada wannan rahoton ba.