✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

’Yan bindiga sun kashe mutum 5 sun raunata wasu a Katsina

’Yan bindigar sun kai a hari a kauyukan Karamar Hukumar Danmusa.

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kauyukan Kanawa da Runka a Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutum biyar.

Wani mazaunin kauyen Kanawa ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai farmaki ne da yamamcin ranar Asabar, lamarin da ya sa mazauna gudun neman tsira.

“Da muka ji karar baburansu nan take muka gudu zuwa cikin daji, amma duk da haka sai da suka bi mu suka kashe mutum shida suka raunata wasu.

“Yanzu (safiyar Lahadi) muka kammala jana’izarsa mutum shida da suka kashe sai kuma mutum uku da suka ji rauni aka kai su asibitin Danmusa suna samun kulawa,” inji shi.

Ya ce ’yan bindiga kusan 60 a kan babura ne suka kai harin da misalin karfe 6:30 na yamma, suka yi awon gaba da dabbobi, mallakin wasu sabbin amare.

Mun tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah kan harin, amma ya ce baturen ’yan sandan yankin bai sanar da su ba, amma ya yi alkawarin bibiyar gaskiyar lamarin.

Harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan dakile wani harin da ’yan bindiga suka kai a kauyukan Wurma da Yabudu da ke Karamar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ya fitar, ta ce, “Da misalin karfe 5:30 na yamma ranar 02/06/2021, ’yan bindiga sama da 150 dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai hari kauyukan Wurma da Yarbudu a Karamar Hukumar Kurfi.

“Jami’an ’yan sanda da ke kauyen Wurma sun yi dauki-ba-dadi da ’yan bindigar, suka kashe daya daga cikinsu tare da raunata wasu da dama, wasu kuma suka tsere suka bar makamansu,” a cewar SP Magaji Isah.

Ya kara da cewa ’yan sandan jihar sun bi sahun maharan har suka yi nasarar kashe hudu tare da kwato babura biyar daga hannunsu.