✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 51 a Zamfara

Mutanen yankunan Zurmi sun tsere saboda tsoron dawowar ’yan bindiga.

’Yan bindiga sun kashe akalla mutum 51 ranar Juma’a a Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

’Yan bindiga sun hallaka mutanen ne a hare-haren da suka kai wa kauyukan Kadawa da Kwata da Maduba da Ganda Samu da Saulawa da kuma Askawa.

“Ana faragbar maharan za su dawo su kashe masu jana’izar wadanda aka kashe, yadda suka yi a baya, shi ya sa aka kai gawarwarkin garin Dauran; Yanzu haka ba mu jima da kammala binne mutum 28 ba”, inji Haruna, mazuanin garin Dauran, inda aka kai gawarwakin. Garin na Dauran na nisan kilomita 10 daga garin Zurmi.

Mazauna kauyukan sun ce gungun barayin dauke da manyan makamai a kan babura sun dirar wa kauyukan nasu ne suna harbin mutane.

Sun kuma yi ta bin mutanen har cikin gidajensu da ma gonakinsu suna ta harbin su.

A halin yanzu daruruwan mazauna kauyukan da ’yan bindigar suka kai wa harin sun tsere.

Yawancinsu, ciki har da mata da yara kanana na neman mafaka a garuruwan Dauran da Zurmi.

Haruna ya shaida wa Aminiya cewa har ya zuwa lokacin hada rahoton nan, akwai gawarwakin wadanda aka kashen da ke yashe a cikin dazukan da ke makwbataka da kauyukan, ko da yake ya ce ana kokarin gano su domin a yi musu jana’iza.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce an gano gawarwaki 14 da za a binne a makabartar Unguwar Gwaza da ke Gusau, babban birnin jihar.

Ya kuma ce kwamishinan ’yan sandan Jihar, Hussaini Rabiu, ya ziyarci kauyen Dauran sannan jami’an tsaro sun kara tsaurara tsaro a yankunan.

Karuwar hare-hare a Zurmi

A makonnin da suka wuce, Karamar Hukumar Zurmin ta fuskanci yawaitar hare-haren ’yan bindiga da ke kashe mutane a yankunan karkara.

Ko a makon jiya wadansu fusatattun matasa sun datse hanyar Gusau zuwa Kaura Namoda da Zurmi, suna maci, kan yawaitar kasha-kashen da ’yan bindiga suke yi a yankin.