✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 6 a sansanin ’yan gudun hijira

Wasu da dama sun jikkata yayin da sauran ke rige-rigen neman tsira da rayukansu.

Da sanyin safiyar Talata ne wasu ’yan bindiga suka kutsa cikin sansanin ’yan gudun hijira na Abagena tare da bindige mutum shida a Jihar Binuwai.

Sansanin ’yan gudun Abagena dai na kan babbar hanyar Makurdi zuwa Lafiya ne a Jihar ta Binuwai.

Mutane da dama kuma sun sami munanan raunuka sakamakon harin, yayin da mazauna sansanin suka rika rige-reigen tserewa domin kubutar da rayuwarsu.

Turmutsitin ya sa dole ababen hawan da ke fitowa da kuma masu zuwa Makurdi suka rika juyawa saboda tsoron abin da ka je ya dawo a kan hanyar.

Muna tafe da karin bayani…