✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 66 a Kebbi

'Yan bindigar sun kashe mutane da dama ciki har da 'yan sanda.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta sanar da cewa mutum 66 ne suka rasa rayukansu a hannun ’yan bindiga a Karamar Hukumar Danko/Wasagu ta Jihar.

Kakakin ’Yan sandan Jihar, DSP Nafiu Abubakar ne ya tabbatar da kisan mutanen da aka yi a ranar Alhamis cikin wasu kauyuka bakwai na Karamar Hukumar.

A cewarsa, ya zuwa yanzu ba a gama kayyade adadin mutanen da suka mutu a hare-haren ’yan bindigar ba, sai dai an aike da karin jami’ai yankunan don tabbatar da tsaro.

Kauyukan da ’yan bindigar suka kai hare-haren sun hada da: Koro, Kimpi, Gaya, Dimi, Zuru, Rafin Gora da Iguenge, duk a Karamar Hukumar Danko/Wasagu ta Jihar.

Aminiya ta gano ragowar mutanen kauyukan da suka tsallake rijiya da baya sun tsere zuwa garin Riba don neman mafaka.

A watan Afrilun da ya gabata ne ’yan bindiga suka kashe ’yan sanda tara, ciki har da Shugaban caji ofis din Danko/Wasagu.