✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 7 a Kaduna

'Yan bindigar sun kai hare-haren ne a kananan hukumomi uku dake jihar.

Rayukan mutum bakwai ne suka salwanta a wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai Kananan Hukumomi uku a Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan inda a cewarsa Kananan Hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Chikun, Giwa da kuma Kajuru.

A cewar Aruwan, daya daga cikin hare-haren ya auku ne a yankin Kan Hawa na Unguwar Zankoro da ke Karamar Hukumar Chikun inda maharan suka far wa motar wasu matafiya.

Kwamishinan ya bayyana cewa maharan sun harbi tayar motarsu, lamarin da ya yi ajalin mutum shida.

Ya bayyana sunayen wadanda suka riga mu gidan gaskiya a harin da suka hada da Aisha Bello, Uwaliya Alhaji Shehu, Ramatu Sani, Muhammad Shehu, Aminu Ibrahim da Ibrahim Abdu.

Sanarwar da Kwamishinan ya fitar ta ce mutum hudu ne suka jikkata sakamakon harin da ‘yan bindigar suka kai yankin Iburu na Karamar Hukumar Kajuru.

Kazalika, ya ce wani dan kasuwa mai suna Alhaji Sule, ya rasa ransa yayin da ‘yan bindigar suka kai hari kauyen Hayin Kanwa da ke gundumar Fatika a Karamar Hukumar Giwa.

Aruwan ya kara da cewa, Gwamna Mallam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana kaduwarsa da wannan hare-hare, inda yake mika sakon ta’aziyyarsa ga ‘yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su.