✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum biyar a Kaduna

'Yan bindigar sun kuma kone gine-gine ciki har da wajen ibada.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum biyar da ’yan bindiga suka kashe a Kananan Hukumomin Chikun da Igabi.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Mista Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a ranar Asabar.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito Aruwan yana cewa, ’yan bindigar sun kashe mutum biyu tare da kone gine-gine ciki har da wajen ibada a Karamar Hukumar Chikun.

Kazalika, ya ce an kashe mutum uku a yankin Lambar Zango da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a Karamar Hukumar Igabi.

Aruwan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana takaicinsa kan aukuwar lamarin tare da aike sakon ta’aziyya zuwa ga ’yan uwan wadanda suka rasu.