✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

’Yan bindiga sun kashe mutumin da suka sace a Binuwai

Wata majiya ta ce an sha kai wa mutanen yankin ire-iren wadannan harin.

Rahotanni sun ce an kashe mutum daya a wani hari da aka kai kauyen Tse-Amee da ke gundumar Mbapa a Karamar Hukumar Gwer a yamma a Jihar Benuwai.

Wani mazaunin kauyen wanda ya bayyana sunansa a matsayin Ibaah, ya shaida mana cewar an sace marigayin, Mista Aza na Tse Amee a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da maharan dauke da makamai suka kai hari kauyen.

Ibaah ya ce daga nan ne maharan suka kashe marigayin bayan sun sace shi.

Sai dai shugaban Karamar Hukumar Gwer West, Andrew Ayande, wanda shi ma ya tabbatar da harin, ya ce an kashe mutumin a ranar Talata a yankin Tse-Amee bayan harin na ranar Lahadi.

“Mutum daya ya mutu, kuma lamarin ya faru ne a ranar Talata, wasu mutane na aikin barar bawon rogo a kauyensu, sai wasu mutane hudu dauke da bindigogi suka farmake su, suka kashe. An yi sa’a ba su kashe macen da ke tare da su ba, sun dai yi mata dukan tsiya.”

Ayande ya ce “An sha samun irin wadannan hare-hare kwanan nan kamar wanda ya faru a Tse-Agagbe a gundumar Sengev da kuma wani a Chile.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP Catherine Anene, ta ce har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai ba ta san da faruwar lamarin ba.