✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe sojoji 7 a Taraba

An kashe su yayin wani kwanton-bauna a Karim Lamido

Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kashe sojoji bakwai a Karamar Hukumar Karim Lamido ta Jihar Taraba.

Aminiya ta gano cewa maharan sun yi wa sojojin kwanton bauna ne a wani daji da ke yankin a ranar Laraba.

Wasu majiyoyi daga yankin sun tabbatar wa wakilinmu cewa sojojin sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke sintiri.

Shugaban Karamar Hukumar ta Karim Lamido, Markus Hamidu, ya tabbatar wa wakilinmu kisan sojojin ta wayar salula a ranar Alhamis.

Ya ce, “Yan bindiga sun kashe sojoji bakwai jiya a kusa da Andami. Wannan abin takaici ne, Allah Ya kare mu.”

Sai dai duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi, kan lamarin ya ci tura saboda wayarsa ta kasance a rufe, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.