✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a Enugu

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan dakarun nata.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun hallaka sojoji biyu a wani artabu da suka yi a yankin Adani na Karamar Hukumar Uzo-Uwani a Jihar Enugu.

Aminiya ta gano cewa sojojin, wadanda aka tura su yankin don su yi yaki da ayyukan ‘yan bindiga, an harbe su ne a wani wurin binciken ababen hawa da ke Iggah/Asabah.

  1. An rufe Jami’ar Legas saboda annobar Coronavirus
  2. Majalisar Kano ta dage zamanta da Muhuyi Magaji

Wani dan asalin yankin da ya zanta da Aminiya ya ce ’yan bindigar sun gididdiba gawarwakin sojojin bayan sun kashe su.

Sai dai bai bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.

Da ya ke mayar da martani game da harin, mai magana da yawun Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birigediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce “An kai hari a kan wasu sojojin Najeriya da aka aike yankin Adani na Karamar Hukumar Uzo-Uwani a ranar 13 ga Yuli, 2021.

“Abun takaici yayin artabu da ‘yan bindigar, sojoji biyu sun rasa rayukansu. Amma dakaru na ci gaba da bincike a yankin.

“Muna bai wa jama’a tabbacin za mu kawo cikakken tsaro tare da hadin gwuiwar wasu jami’an tsaro.

“Sannan muna rokon jama’a da suke bawa jami’an tsaro hadin kai wajen bin doka tare da bada rahoton duk wani wanda ba a yarda da shi ba”.