✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a Sakkwato

Sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin da bakwai suka jikkata.

Sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin da bakwai suka jikkata sakamakon wani hari da ’yan daban daji suka kai Kauyen Lalle da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Aminiya ta samu rahoton cewa, ’yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe biyu na ranar Laraba, inda suka kone wasu motocin sintiri biyu na ’yan sanda da na dakarun sojin kasa.

Majiyar rahoton ta shaida cewa, “sun zo haye a kan Babura 100 kuma a kan kowane babur daya akwai mutum uku wanda kowannesu yana rike da bindiga.

“Sun fito ne daga yankin Tilibale inda suka bude wuta kan sojojin da ke shingen binciken ababen hawa a kan hanyar Sakkwato zuwa Sabon Birni.

“Sojojin sun mayar da martani amma ’yan bindigar suka ci karfinsu saboda yawan da suke da shi,” a cewar majiyar.

Bayanai sun ce an aike da karin motocin soji uku zuwa garin Sabon Birni, amma ’yan bindigar suka yi musu kwanton bauna a kan hanya, inda suka harbe sojoji biyu yayin da wasu bakwai suka tsira da raunuka iri daban-daban.

“A halin yanzu Unguwar Lalle da kewayenta ta zama tamkar Kufai a yayin da jama’a suka tsere saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo, a cewar majiyar.

Majiyar ta ce maharan sun koma yashe kayayyaki a wasu shaguna da ke yankin sannan sun yi awon gaba da dabbobi dama.

Kazalika, sun sace mazauna kauyen da dama ciki har da wani ma’aikacin Asibiti.

Sai dai har yanzu hukumomi basu ce uffan ba a kan lamarin, a yayin da Kakakin Rundunar Sojin Kasan Najeriya, Birgediya-Janar Oneouku ya shaida wa wakilinmu cewa ba shi da labara a kan lamarin.

Haka kuma, neman jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar, ASP Sanusi Abubakar ya ci tura a yayin hada wannan rahoto.