’Yan bindiga sun kashe tsohon Kwamishinan Hukumar Kidaya ta Kasa | Aminiya

’Yan bindiga sun kashe tsohon Kwamishinan Hukumar Kidaya ta Kasa

‘Yan bindiga
‘Yan bindiga
    Umar Muhammad, Lafiya da Sani Ibrahim Paki

Wasu ’yan bindiga sun kashe tsohon Kwamishina a Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Zakari Umaru-Kigbu a Jihar Nasarawa, sannan sun yi awon gaba da ’ya’yansa ’yan mata guda biyu.

Aminiya ta gano cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi a gidan marigayin da ke yankin Azuba Bashayi da ke Karamar Hukumar Lafiya a Jihar.

Kazalika, rahotanni sun ce maharan sun bukaci a ba su Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa kafin su sako wadanda suka kama.

Wani dan uwan mamacin da bai amince a bayyana sunansa ba ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin da safiyar Lahadi.

Ya ce, “Wasu ’yan bindiga sun halaka Zakari jiya da daddare a gidansa da ke Azuba Bashayi da ke Karamar Hukumar Lafiya ta Jihar Nasarawa, sannan suka yi awon gaba da biyu daga cikin ’ya’yansa mata.”

Marigayin, mai shekara 60 dai tsohon sojan sama ne da ya yi ritaya.

Kazalika, binciken Aminiya ya gano cewa kafin kisan nashi, marigayin malami ne a Sashen Koyar da Aikin Jarida na Kwalejin Fasaha ta Isah Mustapha Agwai, kuma tsohon Kwamishinan Tarayyar na NPC ne, mai kula da Jihar Nasarawa.

Bugu da kari, marigayin kafin kisan nashi, shi ne wakilin mai neman takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a jam’iyyar PDP, Labaran Maku, kafin daga bisani ya sauka daga mukamin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu ta wayar salula, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Ramhan Nansel, ya ce sun sami kiran gaggawa me kan lamarin wajen misalin karfe 12:20 na safiyar Lahadi.

Ya ce tuni suka dukufa da bincike don gano yadda lamarin ya faru.

Kakakin ya kuma tabbatar da sace ’yan mata biyu da maharan suka yi a gidan marigayin.

Sai dai ya ce rundunar ba ta sami rahoto kan batun Naira miliyan 50 din da masu garkuwar suka bukata a matsayin kudin fansa ba.