✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga 5 a hanyar Birnin Gwari

’Yan bingida sun yi musu kwanton-bauna yayin da suke dawowa daga Kaduna.

’Yan banga akalla biyar sun kwanta dama bayan ’yan bindiga sun bude musu wuta a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Wani shugaban al’umma a yankin, Liman Husaini Udawa, ya tabbatar wa Aminiya cewa an kai wa ’yan bangar harin ne a kusa da Unguwar Yako da ke kan hanyar.

Ya ce ’yan bangar suna hanyarsu ta dawowa daga Kaduna ne, “’Yan bindiga suka yi musu kwanton bauna suka kona motarsu a kusa da Unguwar Yako a kan babbar hanyar. Yanzu haka mun dauko gawarwakin ’yan banga uku”.

Ya bayyana wa wakilinmu cewa za a binne mamatan a garin Udawa da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Wasu majiyoyi a yankin sun ce an kai wa ’yan bangar farmakin ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Talata.

Mun kisa kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, domin samun karin bayani, amma bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da muka tura masa ba, har muka kammala hada wannan rahoton.