’Yan bindiga sun kashe ’yan banga 5 a Neja | Aminiya

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga 5 a Neja

’Yan bindiga
’Yan bindiga
    Ishaq Isma’il Musa da Abubakar Sadiq Isah

’Yan bindiga sun harbe ’yan banga biyar da mafarauci daya a wani harin kwanton bauna da suka kai dajin da ya ratsa Lafiya zuwa Kpada zuwa Duma a Jihar Neja.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, harin ya jikkatar da wasu ’yan bangar shida da suka samu raunuka daban-daban a sakamakon harbin bindiga.

Wani dan banga da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da rana bayan wasu ’yan banga daga Abuja hadi da wasu daga Jihar Nejan suka shiga dajin domin ceto wasu manoma 22 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Larabar da ta gabata ce wasu ’yan bindiga suka sace manoma 22 ciki har da mutum 13 ’yan gida a kauyen Rafin-Daji da ke Karamar Hukumar Abaji ta babban birnin kasar.

Bayanai sun ce ‘yan banga da mafarauta da suka fita aikin ceto sun tunkari dajin ne, inda bayan cin tafiya mai tazarar gaske sai ‘yan bindigar da suka yi kwanton bauna suka bude musu wuta.

Majiyar ta ce wasu daga cikin yan bindigar da suka shammaci yan bangar sun buya ne a saman bishiya, inda suka rika yi musu ruwan harsashi, lamarin da ya yi ajalin biyar daga cikinsu da kuma wani mafarauci daya.

“’Yan bangar biyar da mafaraucin sun mutu ne a sakamakon zubar jini mai yawan gaske, la’akari da cewa babu wadatacciyar hanyar da za a yi gaggawar mika su asibiti,” a cewar majiyar.

Wakilinmu da ya ziyarci sashin masu hadarurruka da bukatar agajin gaggawa na Babban Asibitin Abaji, ya ga ’yan bangar shida da suka jikkata ana kula da su, yayin da ’yan uwa da abokan arziki ke jajanta musu.

Wani bincike ya tabbatar da cewa maboyar ’yan bindigar tana nan a wani daji da ke Karamar Hukumar Lapai ta Jihar Neja wanda yake iyaka da garin Yaba na Karamar Hukumar Abaji ta Abuja.

Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, ASP Oduniyi Omotayo, bai ce uffan ba game da lamarin, domin har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai amsa sakon da aka aika masa ba.