✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar ‘yan bangar da ‘yan bindiga suka kashe

An yi jana’izar ‘yan bangar da ‘yan bindiga suka bude musu wuta a lokcin da suke kokarin kwato mutanen da ‘yan bangar suka yi garkuwa…

An yi jana’izar ‘yan bangar da ‘yan bindiga suka bude musu wuta a lokcin da suke kokarin kwato mutanen da ‘yan bangar suka yi garkuwa da su.

‘Yan bindigar sun yi garkuwa da mutum 30 bayan sun shafe awanni suna cin karensu babu babbaka a Karamar Hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa.

“Mun binne ‘yan banga guda biyu da ‘yan bidiga suka kashe a kan Dutsen Onda”, inji shugaban karamar hukuman, Muhammad Otto.

Mazauna sun ce maharan kimanin su 50 a kan babura sun tare hanyar Udege zuwa Loko na awanni inda suka kwashi mutanen a cikin daren Litinin.

Otto ya ce, “‘Yan bindigar sun kashe ‘yan banga guda biyu a kan Dutsen Onda, a kwaton baunar da suka yi wa ‘yan bangar da suka bi su domin kwato mutanen aka yi garkuwa da su”.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ASP Nansel Ramhan bai amsa kiran wakilinmu ba domin karin bayani.