✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 10 a Burkina Faso

Har yanzu ba a ga wasu dakaru da dama ba.

Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayakan jihadi ne sun kashe ’yan sanda 10 a Arewacin kasar Burkina Faso da ke kusa da iyaka da Nijar.

Wata majiya ta ce, “a daren ranar Alhamis ne ’yan ta’adda suka kai hari a wani sansanin Jandarma [’Yan sanda] a Seytenga da ke Lardin Seno.”

Majiyar ta kara da cewa “Kimanin jandarmomi [’Yan sanda] 10 sun mutu, hudu sun samu raunuka, an kuma yi barna sosai,” akwai yiwuwar adadin ya karu inji majiyar.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da harin, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren zubar da jini a kasar Burkina Faso.

A cewarta, jami’an tsaro sun fatattaki maharan a wani hari da suka kai musu, inda a yanzu haka suke farfasa wurin.

“Har yanzu ba a ga wasu dakaru da dama ba” har zuwa safiyar Juma’a,” in ji majiyar ta biyu.

Daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, Burkina Faso ta fada cikin rikici na kusan shekaru bakwai da mayakan jihadi suka tsallaka daga makwabciyar kasar Mali.

Wannan harin dai ya faru ne bayan wani harin a ranar Alhamis ya kashe jami’an tsaro a Yammacin Lardin Kossi da wani hari a mahakar zinari a Arewacin kasar kamar yadda DW ya ruwaito.

Hare-haren ’yan ta’adda a Burkina Faso ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 2,000, a yayin da kusan mutane miliyan 2 sun tsere wa gidajensu sakamakon ayyukan ta’addanci musamman a arewacin kasar.