✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 2 a Sakkwato

Rundunar 'yan sandan Jihar Sakkwato ta tabbatar da kisan wasu 'yan sanda biyu da 'yan bindiga suka yi a kauyen Bargaja.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta tabbatar da kisan wasu ’yan sanda biyu da wasu ’yan bindiga suka yi a kauyen Bargaja dake jihar.

Kazalika, wani rahoto ya ce karin wasu mutum a kauyen sun rasa rayukansu yayin da ’yan bindigar suka kai farmaki kauyen a ranar Litinin.

A cewar wani mazaunin yankin, “Sun tarar da mutanenmu a gona suna aiki, kuma nan take suka harbe su.

“Muna jin karar harbin bindiga, nan take muka sanar da jami’an ’yan sandan, kan su kawo mana dauki.

“Lokacin sun yi arba da ’yan sanda an yi musayar wuta sosai, wanda a sanadin hakan suka kashe ’yansanda biyu, amma ban sani ba ko su ma an kashe musu mutane, saboda ba su bar gawar ko mutum ko daya ba,” inji majiyar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da rasuwar ’yan sandan, sai dai bai yi cikakken bayani ga wakilinmu kan lamarin ba.

Sai dai ya yi alkawarin kiran wakilinmu don ba shi cikakken bayanin yadda lamarin ya auku a nan gaba.