✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

’Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 3 a Ebonyi

An harbe 'yan sandan ne yayin da suke bakin aiki

’Yan bindiga sun harbe wasu ’yan sanda uku da bindiga har lahira ranar Asabar a Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Chris Anyanwu, shi ne ya tabbatar da aukuwar hakan ranar Lahadi Abakaliki.

“’Yan bindigar sun zo ne a cikin motoci biyu inda suka ritsa ’yan sandan a bakin aiki a shingen bincike suka bude musu wuta.

“’Yan sanda uku ne suka samu mummunan rauni yayin harin wanda daga bisani aka tabbatar da sun riga mu gidan gaskiya,” in ji Anyanwu.

Ya ce harin ya auku ne a wani kauye da ke kan iyakar Jihar Ebonyi da Enugu.

(NAN)