✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a Taraba

Wasu ’yan bindiga sun bindige wasu jami’an ’yan sanda biyu a Karamar Hukumar Karim Lamido ta Jihar Taraba. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP David…

Wasu ’yan bindiga sun bindige wasu jami’an ’yan sanda biyu a Karamar Hukumar Karim Lamido ta Jihar Taraba.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP David Misal ne ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce an kashe ’yan sandan ne a bakin aikinsu.

Aminiya ta ruwaito cewa an harbe ’yan sandan ne da misalin karfe 7 na Yammacin ranar Litinin yayin da motarsu ta sintiri ta lalace a kwanar Jen da ke yankin na Karim Lamido.

Lamarin ya wakana ne a yayin da ’yan sandan ke kokarin gyara motar sai kwatsam ’yan bindigar haye a kan babur suka bude musu wuta inda biyu daga cikinsu suka mutu nan take.

Kazalika, ’yan bindigar sun tsere da bindigu biyu na ’yan sandan da suka kashe sannan suka koma cikin jejin da suka fito.

Kisan jami’an ’yan sandan biyu na zuwa ne bayan kwanaki uku da wasu ’ya bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka kashe Shugaban Karamar Hukumar Ardo-Kola mai suna Salihu Dovo da dan uwansa Timothy Aminu a birnin Jalingo.

Aminiya ta ruwaito, rundunar ’yan sanda a Jihar Filato ta kashe wasu mutum biyu da ake zargi da ta’adar garkuwa da mutane a garin Gindiri na Karamar Hukumar Mangu ta jihar.

ASP Ubah Ogaba, jami’in hulda da al’umma na rundunar, shi ne ya inganta rahoton cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a birnin Jos.