✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sa cikina ya zube —Dalibar Afaka

Sau uku ina sumewa, ’yan bindiga na ba ni magani. Zannuwan jikinmu muke yagawa muna kunzugu.

Wata matar aure daga cikin Dalilai 27 na Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka a Jihar Kaduna da aka sako, ta ce wuyar da suka sha a hannun masu garkuwar ta sa juna biyun da take dauke da shi ya zube.

Fatima Ibrahim Shamaki, ta shaida wa Aminiya cewa duk da wahalar da ta sha a lokacin da cikin nata ya zube, ta ki bayyana halin da take ciki domin ta samu ta tsira da rayuwarta.

An tsinci gawar dalibi a Kano bayan kwana 5 da batansa

Najeriya za ta fara gurfanar da masu taimaka wa ta’addanci a gaban kotu —Malami

Ta ce, “Ina tsoro saboda a duk lokacin da wani daga cikinmu ya ce musu ba shi da lafiya, sai su nuna za su ‘karasa’ shi. Shi ya sa nake ganin idan suka san halin da nake ciki za su iya cutar da ni.”

Matar auren, wadda mahaifinta ya rasu a lokacin da take hannun ’yan bindiga, ta ce masu garkuwar na  tambayar mata daga cikin dalilan ko a cikinsu akwai mai ciki, amma ta ki bayyana kanta saboda ba ta san abin da zai iya faruwa ba.

Fatima ta ce, a lokacin da cikin nata mai wata biyu ya bare, “Matan cikinmu ne suka rika taimaka min. Muna taimaka wa juna, idan haila ya zo wa wata a cikinmu mukan yaga zannuwanmu mu ba ta ta yi kunzugu.”

A hirar da Aminiya ta yi da ita bayan Gwamnatin Jihar Kaduna ta mika su ga iyalansu, Fatima ta ce ta yi rashin lafiya mai tsanani a lokacin da suke hannun ’yan bindigar a cikin daji.

Ta ce sau uku tana sumewa, a wasu lokutan ma ’yan bindigar ke ba ta magungunan rage radadi, ganin irin kurmususun da take yi saboda tsananin ciwon ciki.

Matar ta ce, a lokacin da ’yan bindigar suka tafi da su, sai da suka yi kusan awa shida suna tafiya a kafa a cikin kungurmin daji.

Ta ce sau hudu ana canza wurin da aka boye su, baya ga zagi da azabtarwar da aka yi ta musu, kodayake babu wadda aka yi wa fyade a cikinsu.

“A fili muke kwanciya a karkashin bishiyoyi, muna ganin birai da kuraye. Akwai kuma shanu, amma na ’yan bindigar ne,” kamar yadda ta bayyana.