✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da babban basarake na Masarautar Ankpa a jihar Kogi, Alhaji Shu’aibu Usman. Alhaji Usman wanda shi ne mai rike…

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da babban basarake na Masarautar Ankpa a jihar Kogi, Alhaji Shu’aibu Usman.

Alhaji Usman wanda shi ne mai rike da kambun sarautar Eje na Ankpa kuma Darakta a Karamar Hukumar Ankpa, ya fada tarkon ’yan bindigar ne da misalin karfe 5.30 na safiya yana zummar shiga masallaci domin sallar Asuba.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ayuba Edeh, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zanta wa da manema labarai a ranar Juma’a cikin birnin Lakwaja, inda ya ce bas u ga ta zama ba har sai wadanda suka aikata ta’asar sun shiga hannu.

Ya ce an yi wa yankin na Ankpa tsinke da jami’an tsaro a duk wata mashiga da mafita don ganin an ceto Basaraken.

Da yake magana dangane da lamarin, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Kingsley Fanwo, ya ce za su yi iyaka bakin kokarinsu don tabbatar da an ceto Basaraken cikin koshin lafiya.

A cewarsa, “Gwamnatin jihar tana ci gaba da aikin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar an ceto Basaraken cikin lokaci mai takaitaccen zango.”