✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace basarake a Zamfara

Mun yi matukar kaduwa, mutane suka yi ta gudun tsira da ransu.

’Yan bindiga sun sake kai hari garin Adabka da ke Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, inda suka sace hakimin yankin, Alhaji Nafiu Shehu.

Bayanai sun ce maharan sun kai farmakin ne a ranar Asabar da misalin karfe 12 na rana har zuwa 4 na yamma.

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa manema labarai cewa ’yan bindigar sun dirar wa fadar dagacin tare da masu yi masa hidima.

Zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Zamfara ba ta tabbatar da kai harin ba.

Sai dai majiyar rahoton ta tabbatar da aukuwar lamarin da ya kai ga sace basaraken.

“Abin mamaki ne, yadda ’yan bindiga suka shiga har fadar mai martaba da masu yi masa hidima ba su saci kowa ba bayansu kuma ba su kashe kowa ba.

“Mun yi matukar kaduwa, mutane suka yi ta gudun tsira da ransu lokacin da suka ga ’yan bindigar dauke da AK-47 amma ba su taba kowa ba….” in ji mutumin da ya ga faruwar lamarin.