✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace dagaci a Katsina

Mazauna kauyen sun gaza ankarar da jami’an tsaro saboda rufe layukan sadarwa.

’Yan bindiga sun sace dagacin kauyen Banye da ke Karamar Hukumar Charanchi a Jihar Katsina.

Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindiga sun yi awon gaba da dagacin kauyen mai suna Alhaji Bishir Gide Banye tare da wani dalibin makarantar sakandire guda daya.

Wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun far wa kauyen a cikin daren ranar Juma’a kuma kai tsaye suka nufi gidan dagacin inda suka yi awon gaba da shi.

Banye na daga cikin kauyukan Karamar Hukumar Charanchi da katse layukan sadarwa ta shafa saboda kusancinsa da Karamar Hukumar Kurfi.

Bayanai sun ce hakan ne ya bai wa ’yan bindigar damar kai harin ba tare da fuskantar wani kalubale duba da cewar babu yadda za a yi mazauna kauyen su iya ankarar da jami’an tsaro.

Wannan shi ne karo na biyu da aka sace dagaci a Jihar Katsina, inda a bayan nan mahara suka yi awon gaba da dagacin kauyen Barkiya na Karamar Hukumar Kurfi.

Sai dai ya tsallake rijiya da baya sakamakon ankarar da jami’an tsaro da aka yi wanda cikin gaggawa suka bi sahun maharan suka ceto shi.

Da aka tuntubi Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah domin jin karin bayani, ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba kuma ya sha alwashin waiwayar wakilinmu da zarar an kawo rahoton hedikwatar ’yan sanda ta jihar.