✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace dalibai 15 da malamai 5 a kwalejin Zamfara

An kai harin ne a Kwalejin Koyon Aikin Gona da ke Karamar Hukumar Bakura.

Wasu ’yan bindiga sun kai hari Kwalejin Koyon Aikin Gona da Kimiyyar Dabbobi da ke Karamar Hukumar Bakura a Jihar Zamfara inda suka sace dalibai 15 da malamai biyar.

Harin dai na zuwa ne kasa da mako biyar bayan an sace Shugaban makarantar, amma aka sako shi daga bisani bayan biya kudin fansa.

Wani ma’aikacin makarantar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan dauke da makamai sun kusta kai cikin makarantar da misalin karfe 11:na daren ranar Lahadi ta wata karamar kofa, sannan suka tunkari dakunan kwanan dalibai.

A cewar majiyar, “Lokacin da suka shigo, ’yan sandan da aka ajiye suna gadin makarantar sun yi musayar wuta da su. An dada tsaurara matakan tsaro lokacin da ’Yan Sa-kai suka zo daga yankunan da ked a makwabtaka da makarantar.

“Amma duk da haka, ’yan bindigar sun ci karfin ’Yan Sa-kan da jami’an ’yan sandan, watakila saboda sun fi su yawa da kuma makamai.

“Sun rika shiga daki-daki suna balle kofofi suna zakulo dalibai. Sun rika nuna musu bindiga ta tagogi suna musu barazanar ko su bude kofa ko a kashe su.

“Daga bisani sun kira Shugaban kwalejin inda suka shaida masa cewa sun sace mutum 20. Sai dai har yanzu ba su bukaci kudin fansa ba tukunna.

Sai dai yunkurinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu kan harin ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.