✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace dalibai a Kudancin Kaduna

An kai harin ne wajen karfe 10:00 na dare, inda aka sace dalibai da dama.

Wasu ’yan bindiga da ake kyautata masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wasu dalibai a makarantar St. Albertine Seminary da ke Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna.

Majiyar Aminiya ta ce, maharan na shiga kauyen Fayit, inda makarantar, wadda mallakin cocin Katolita ce take, suka fara harbe-harbe, kafin daga bisani su tafi da wasu daliban.

“Ban san adadin daliban da aka sace ba, amma tabbas sun tafi da wasu. Sun shigo ne suna harbe-harbe, suka rikita mutanen wajen kafin su samu nasarar abin da ya kawo su,” inji majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta.

Majiyar ta ce maharan sun yankin da ke Masarutar Fadan Kagoma ne da misalin karfe 10:00 na dare kafin wayewar garin Talata.

Sai dai kokarin Aminiya na jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ci tura domin bai dauki wayar wakilinmu ba yayin da ya kira, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.