✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace dalibai, sun harbi wasu a Kebbi

Sun kashe jami'an tsaro masu gadin makarantar, suka yi wa dalibai luguden wuta.

’Yan bindiga sun sace dalibai da dama bayan sun harbi wasu daga cikin daliban a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yauri, Jihar Kebbi.

’Yan bindiga sun kai wa kwalejin harin ne da tsakar ranar Alhamis, suka bindige mai gadin makarantar kafin su yi awon gaba da dalibai masu tarin yawa, kamar yadda wasu mazauna suka tabbatar.

“Sun ci karfin ’yan sandan Mobile da ke gadin makarantar wadanda sun fi 20, sun sassari wasu sannan suka harbi wasu; Akwai ’yan sandan da aka sara an tafi da su asibiti, yayin da su kuma ’yan bindigar suka wuce da wasu yara,” kamar yadda BBC ta ruwaito dan Majalisar Tarayya mai wakiltar yankin, Muhammad Bello Ingaski.

Mutanen garin Yauri sun ce a lokacin harin, ’yan bindiga sun harbi dalibai da dama da suka yi yunkurin tserewa.

Bayan tafiyar maharan da dalibai maza da mata da suka dauke, an garzaya da daliban da suka samu raunukan harbi zuwa asibiti domin ba su kulawa.