✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace daliban jami’a a Abiya

Har yanzu ba a tantance adadin daliban da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su ba.

Gwamnati a Jihar Abiya ta sanar da cewa ’yan bindiga sun yi awon gaba da wani adadi na daliban jami’ar jihar ABSU a daren ranar Larabar da ta gabata.

Wata sanarwa da Kwamishinan Labaran Jihar, John Kalu ya fitar a ranar Alhamis, ta ce ’yan bindigar sun yi wa daliban kwanton bauna ne yayin da suke tafiya a cikin motarsu a kan hanyar Okigwe zuwa Uturu.

Sai dai ya har yanzu ba a iya tantance adadin daliban da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su ba.

“Bayanan farko da muka samu sun nuna cewa daliban suna tafiya ne a cikin wata karamar mota ta bas daga Okigwe zuwa Uturu da misalin karfe 7 zuwa 8 na dare yayin da suka ci karo da ’yan bindigar wadanda suka tisa keyarsu zuwa dokar daji.

“Biyu daga cikin daliban sun yi nasarar tserewa daga hannun maharan yayin da ragowar ke tsare a hannunsu a wani boyayyen wuri.

“Muna ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Jihar Imo da kuma hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki na jihohin biyu domin tabbatar da an kubutar da daliban da aka sace.

“Sannan muna shawartar al’umma da sauran daliban jami’ar ABSU da su kwantar da hankalinsu domin ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ceto wadanda abin ya shafa cikin koshin lafiya.

“Ba za mu bari masu aikata laifi a tsakaninmu su ketare fushin doka ba a yayin da muka dauki aikin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Abiya da maziyarta jihar da matukar muhimmanci,” a cewar Kwamishinan.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Larabar da ta gabata ce ’yan bindigar da suka sace daliban Kwalejin Noma da Ganduj Daji da ke Afaka a Karamar Hukumar Igabin Jihar Kaduna sun saki ragowar dalibai 27 da suka yi garkuwa da su.

Sako daliban na zuwa kasa da sa’a 24 bayan da a ranar Talata iyayen daliban suka gudanar da zanga-zangar neman a shiga lamarinsu a harabar ginin Majalisar Dokokin Tarayya da ke Abuja, babban birnin kasar.