✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace dan kasuwa da dansa a Jalingo

’Yan bindigar kimanin mutum 10 sun kai hari masallacin Jalo da ke unguwar Saminaka,

Wasu ’yan bindiga sun harbe mutum guda tare da sace wani dan kasuwa da dansa yayin da suka kai hari wani masallaci a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Da misalin karfe 7:00 na daren ranar Alhamis ne dai ’yan bindigar kimanin mutum 10 suka kai hari masallacin Jalo da ke unguwar Saminaka, inda suka kashe wani mai suna Babangida.

Rahotanni sun bayyana cewa, a baya-bayan nan ’yan bindiga sun harbe mutane da dama, ciki har da wani dan sanda yayin da suka sace kimanin mutane 30 – ciki har da mata hudu.

’Yan bindigar dai na tsallakowa ne daga tsaunikan da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola, kusa da yankin da suka kori mutane.

A hannu guda kuma, mun yi yunkurin ji ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, sai dai hakan ya ci tura, kasancewar wayarsa na kashe lokacin da wakilinmu ya lalube shi a waya.