’Yan bindiga sun sace DPO a Kaduna | Aminiya

’Yan bindiga sun sace DPO a Kaduna

Jami’in dan sanda
Jami’in dan sanda
    Ishaq Isma’il Musa da Mohammed I. Yaba

’Yan bindiga sun yi awon gaba da wani DPO din ‘yan sanda da aka tura aiki kwanan nan zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

An sace DPO din ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 9 na safe a ranar Litinin.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa DPO din na kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari ne domin kama sabon aikinsa a lokacin da lamarin ya faru.

Sai dai kawo yanzu babu tabbaci ko jami’in na tafiya ne shi kadai a cikin motar lokacin da aka dauke shi ba.

Har yanzu dai ’yan sanda ba su ce uffan ba ballantana fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Da aka tuntubi Mohammed Jalinge, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ya ce, “Zan binciko lamarin tukunna.”