✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace DPO a Nasarawa, sun nemi N5m kudin fansa

An sace shi lokacin da yake tsaka da farautar ’yan bindiga

’Yan bindiga sun sace baturen ’yan sanda (DPO) na Karamar Hukumar Nasarawa-Eggon a Jihar Nasarawa, CSP Haruna Abdulmalik, a kan hanyarsa ta ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

An sace shi ne lokacin da yake aikin sintiri a kan hanyar Nasarawa-Eggon zuwa Akwanga da daren Laraba.

Ya dai hadu da masu garkuwar ne a kan hanya, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi, kafin su yi awon gaba da shi zuwa wajen da ba a kai ga tantancewa ba.

Rahotanni sun ce DPOn dai ya sami bayanai kan yadda maharan suka hana yankin sakat, inda ya gamu da nashi iftila’in a kokarinsa na dakile su.

A cewar wata majiya a yankin, “Muna cikin takaicin cewa an sace DPO. Tun da aka turo shi yankinmu yake ta kokarin ganin ya fatattaki ’yan bindiga da ragowar bata-gari.

“Bayanan da muka samu sun nuna cewa yana kokarin lalubo bakin zaren wata matsala ce saboda ’yan bindiga sun addabi wajen, sai aka sace shi, abin takaici.

“Mun kuma ji labarin cewa sun kira iyalansa suna neman miliyan biyar a matsayin kudin fansa.

“Muna kira ga Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Nasarawa da ta tabbata an sako shi ba tare da ko kwarzane ba, sannan a kama masu hannu a ciki,” inji majiyar.

Da yake tabbatar da labarin ga wakilinmu, Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa-Eggon, Mista Benjamin Kuze, ya ce lamarin ya faru ne wajen karfe 9:00 na daren Laraba.

“Mun kai rahoto ga Rundunar ’Yan Sanda a kan lamarin, kuma na tabbatar tana iya kokarinta wajen kubutar da shi,” inji Mista Benjamin.